Connect with us

Politics

Atiku Ya Bukaci Yin Sabuwar Maja Domin Tunkarar Jam’iyyar APC A 2027

Published

on

Tsohon mataimakin shugaban kasa , Atiku Abubakar

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

 

Advertisement

Tsohon mataimakin shugaban kasa , Atiku Abubakar ya ce yana da yakinin cewar hadewar jam’iyyun hamaiyya wuri daya zai temaka wajen kafa wata babbar jam’iyyar da zata kalubalanci jam’iyyar APC mai mulkin kasa.

Atiku wanda ya kasance dan takarar shugaban kasa a zaben da ya gabata karkashin jam’iyyar PDP, ya baiyana haka ne a Abuja a jiya a lokacin da ya karbi bakuncin yan gudanarwar majalisar bada shawarwari a tsakanin jam’iyyu.

Advertisement

Sojoji sun kashe ‘yan bindiga biyu, sun kwato makamai a jihar Kaduna

Atiku ya koka ka salon takun jam’iyyar APC a kasar nan wadda take neman komawa salon tsarin mulkin kama karya, a saboda haka ne ya yi kira ga yan kungiyar dasu bada shawarar yadda za’a kafa wata babbar jam’iyayr guda daya domin Maja.

Yan kungiyar sun kai ziyarar ne bisa jagorancin shugabansu na kasa Yabagi Sani.

Advertisement

A wani labarin kuma Sojoji sun kashe ‘yan bindiga biyu, sun kwato makamai a jihar Kaduna

Gwamnatin tarayya ta ce yanzu haka shirye-shirye sunyi nisa domin sauya akalar motoci har milyan 10 masu amfani da man fetir zuwa amfani da Gas nan da watanni 36 masu zuwa.

Advertisement

Karaminin ministan Mai, Ekperikpe Ekpo ne ya baiyana haka a yayin baje kolin mai da iskar gas na shekarar bana wanda ake gudanarwa a birnin Abu Dhabi na hadaddiyar daular larabawa.

A wata sanarwa da kakakinsa Louis Ibah ya fitar, ya baiyaan cewar a yanzu haka anyi kawance da kanfanoni masu zaman kansu domin kawo kayayyakin da za’a yi amfani dasu wajen sauya akalar motocin nan da watanni 9 masu zuwa.

Advertisement

Ya ce matakin wani yunkuri ne na inganta yin amfani da Gas a tsakanin motocin kasar a maimakon Man fetir da suka dogara dashi.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending