Politics
NNPP Ta Dakatar Da Shugaban Karamar Hukumar Birni Da Mataimakinsa
Jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) reshen jihar Kano ta sanar da dakatar da shugaban jam’iyyar na Karamar Hukumar Birni, Hon. Ibrahim Rabi’u Change, da mataimakinsa, Hon. Zakari Mamuda Koki, na tsawon watanni shida, bisa zargin karya dokokin jam’iyya da rashin nuna kwararan halayen jagoranci.
Sanarwar dakatarwar na kunshe ne cikin wata takarda da Mataimakin Sakataren Yaɗa Labarai na jam’iyyar, Sadik Adam Danba’ura, ya fitar a ranar Asabar, bayan kammala wani taron gaggawa da aka gudanar a sakatariyar jam’iyyar da ke Sharada.
Rikici Na Kara Kamari A Majalisar Tarayya Kan Mulkin Shugaba Tinubu
A cewar Danba’ura, cikin mambobin kwamitin zartaswa 28 da ke jam’iyyar a karamar hukumar, mutum 22 ne suka goyi bayan daukar matakin dakatarwar, wanda aka bayyana a matsayin matakin ladabtarwa da gyaran fuska ga shugabannin da suka gazawa al’umma da jam’iyya.
Ya ce, “Bincike da shaidun da muka samu sun nuna cewa shugabannin biyu sun kasa gudanar da ayyukansu yadda doka da tsarin jam’iyya suka tanada. Hakan ya janyo gazawar jam’iyya a matakin ƙasa da kuma ɓacin ran mambobi da dama.”
Jam’iyyar ta ce gazawarsu ya hada da nuna halaye marasa da’a, kin girmama manyan jagorori, da kuma nuna wariya da rashin nuna kishin jam’iyya.
Duk da daukar matakin dakatarwa, har yanzu ba a fitar da sunayen wadanda za su rike mukaman shugaban jam’iyyar da mataimaki a matsayin na wucin-gadi ba, sai dai jam’iyyar ta tabbatar da cewa an kaddamar da bincike mai zurfi domin tsaftace shugabancin a matakin ƙaramar hukuma.
