Connect with us

Politics

SIYASAR Kano: Kotun daukaka kara ta yanke hukunci na wucin gadi ne – Jigon NNPP

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

 

Advertisement

Wani jigo a jam’iyyar New Nigeria Peoples Party, NNPP, Ambasada Olufemi Ajadi Oguntoyinbo ya bayyana hukuncin kotun daukaka kara da ke zamanta a Abuja da ta kori gwamnan jihar Kano Abba Yusuf a matsayin koma baya na wucin gadi.

Oguntoyinbo ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a kamar yanda jaridar Daily Post ta ruwaito

Advertisement

Gwamnonin arewacin Kasar nan na neman tallafin noma daga bankin raya Afirka

Jaridar Inda Ranka ta ruwaito cewa kotun daukaka kara a ranar Juma’a ta tabbatar da hukuncin kotun da ta bayyana dan takarar jam’iyyar All Progressives Congress, Nasiru Gawuna a matsayin wanda ya lashe zaben gwamna.

Shugaban jam’iyyar NNPP a wata sanarwa da ya fitar ga DAILY POST, ya ce, “Na samu labarin hukuncin na ranar juma,a a matsayin rashin kunya. Amma ina ganin shi a matsayin koma baya na wucin gadi saboda hukuncin ba zai iya jurewa nan da wani lokaci.

Advertisement

“Abin mamaki ne yadda hukuncin kotunan biyu ya bambanta. Yayin da kotun da ke karkashin mai shari’a Oluyemi Osadebay ta soke zaben gwamna Abba Yusuf inda ta bayyana kuri’u 165,663 marasa kyau.

 

Advertisement

“Kotu ta tabbatar da cewa ba hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa ta sanya hannu ba kuma ba ta buga tambari ba. Kotun daukaka kara a hukuncin da ta yanke ta ce Yusuf ba ya cikin rajistar zama mamba na jam’iyyarsa ta siyasa.

 

Advertisement

“Wannan abin mamaki ne, a ce dan takarar jam’iyyar da ya yi yakin neman zabe a lungu da sako na jihar kuma jama’a suka zabe shi da yawa ba dan jam’iyyar ba ne.

“Na roki mai girma Gwamna Abba Yusuf da ya kwantar da hankalinsa, domin wannan hukunci ba zai iya jure wa ba. Na kuma yi alkawari da dan takararmu na shugaban kasa, Sanata Rabi’u Musa Kwakwanso da mu kwantar da hankalinmu, sannan na bukaci magoya bayanmu a fadin kasar nan da su kwantar da hankalinsu.”

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending