Politics
PDP Ta Nemi Buhari da ya tilasta wa ‘yan APC su Saki Sabbin Kudin Da Su Ka Boye
Jamiyyar PDP, ta yi kira ga Shugaba Muhammadu Buhari ya tilasta wa ‘yan jam’iyyar APC da gwamonin ta da Bola Ahmed Tinubu, su fito da biliyoyin sabbin takardun kudin da su ka boye domin sayen kuri’u.
PDP ta yi kiran ne a cikin wata sanarwa da kakakin ta na kasa Debo Ologunagba ya fitar, biyo bayan karancin sabbin takardun kudaden da ake ci-gaba da fuskanta a daukacin fadin Nijeriya.
An baza ƴan sanda a Lagos domin daƙile zanga-zangar ƙarancin Kudi
Ologunagba, ya ce a jawabin da shugaba Buhari ya yi wa ‘yan Nijeriya ya sanar da cewa, tsarin sauya kudaden, tsarin gwamnatin APC ne da ke sa ido a kan yadda ake sarrafa sabbin kudaden da kuma zagayawar su a cikin al’umma.
Ya ce hakan ya nuna a zahiri babu hannun jamiyyar PDP a cikin wannan tsarin, ya na mai cewa tun a baya PDP ta ankarar da ‘yan Nijeriya a kan zagon kasan da ake yi na karkata sabbin takardun kudaden domin cimma burin shirin su na cin zabe.
Ologunagba, ya ce PDP ta na tausaya wa ‘yan Nijeriya a kan wannan karancin sabbin takardun kudaden da su ke ci-gaba da fuskanta, inda ya ce PDP ta tona asirin gwamnonin APC bisa zargin su da boye sabbin kudaden a wata maboyar da ke jihohin Legas da Kano da Kogi da Kaduna da Imo, domin kawai su sayi kuri’un mutane a zabe mai zuwa.
