Politics
Wadanda aka yi canjin kudin domin su, ko a jikinsu-Kwankwaso
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
‘Yan takarar shugaban ƙasa bankunan ƙasar nan mallakinsu ne don haka ba abin da ya dame su da ƙaramcin kuɗaɗe da yake damun wasu ‘yan Nijeriya a yanzu haka
Kwankwaso yabaiyana hakan ne yayin tattaunawa da gidan talabijin na Channels a cikin shirin Sunrise Daily, ya bayyana cewa, “yawancin masu hannu da shuni da waɗannan ‘yan takara su ne masu ruwa da tsaki na bankunan nan. Don haka ba ruwansu da rashin kuɗaɗe a hannun jama’a.
Mu a jam’iyyar NNPP ba mu ji dadin abin da ya faru ba kuma ba ma jin dadin abin da ke faruwa a yanzu haka, game da wannan rashin kuɗi da ake fama da shi.
Wa’adin watannin ukun da aka bayar da karin kwanaki goman dukkansu ya kamata a ce an yi nazari a kansu da kyau. Domin yawan wadanda suka aiwatar da wannan tsari suna can ne a Abuja suna zaune a ofisoshinsu ba su san halin da jama’a suke ciki ba”.
