Sports
Kocin Arsenal ya ce dole ne tawagarsa ta kara azama idan tana so ta ci gaba da samun nasarori a wasanni .
Kocin Arsenal, Mikel ArtMikel Arteta eta ya ce dole ne tawagarsa ta kara azama idan tana so ta ci gaba da samun nasarori a wasanni .
Dan wasan bayan Faransa, William Saliba ne ya fara ci wa Arsenal kwallo kafin daga bisani Sportin Lisbon su yi amfani da kurakuran masu tsaron baya su saka musu kwallaye biyu ta hannun Goncalo Inacio da Paulinho.
Dan wasan baya na Sporting Lisbon, dan kasar Japan, Hidemasa Morita ne ya ci gida, lamarin da ya sa Arsenal suka dawo cikin wasan gabanin haduwa ta 2 da za su yi a Alhamis mai zuwa a filin wasa na Emirates.
Sai dai hakan bai yi wa Arteta dadi ba, duba da yadda tawgarsa ta bari aka saka mata kwallaye 2 a raga a cikin wasa na 2 a jere.
Ya ce duk inda tawaga ta bari aka saka mata kwallaye biyu a raga, to lallai ta shiga loko Kenan.
