Sports
An haramta wa Ahmed Al-Saleh kwallo har abada
Hukumar ƙwallon kafa ta kasar Syria ta haramta wa tsohon kyaptin ɗin ƙkasar, Ahmed Al-Saleh ƙwallo har abada bayan da ya kwarfa
tare da cin zarafi har ma da tafowa alƙkalin wasa yawu.
Ɗdan wasan ma shekara 33, dan wasan baya na ƙdungiyar Al-Jaish ya nuna fushinsa kan alƙkalin wasan bayan da ya nuna masa jan kati yayin wasansu da Al-Wathba a ranar Juma’a.
Lamarin dai ya sa ƴdan wasa daga duka ɓangarorin rirrike Al-Saleh a lokacin da ya fusata.
Kwamitin ladabtarwa na hukumar ta kuma ci tarar ɗan wasan da Al-Jaish, waɗanda kuma ba za su iya ƙkalubalantar hukuncin ba.
Hukumar ƙkwallon ƙkafar ta Syria ta ce Al-Saleh ya ci gaba da zagin alƙkalin wasan har bayan da suka koma wajen canja kaya.
Advertisements
