Connect with us

Sports

Kocin Arsenal ya ce dole ne tawagarsa ta kara azama idan tana so ta ci gaba da samun nasarori a wasanni .

Published

on

Kocin Arsenal, Mikel ArtMikel Arteta eta  ya ce dole ne tawagarsa ta kara azama idan tana so ta ci gaba da samun nasarori a wasanni .

Advertisements
Advertisements
Ya yi  wannan bayani ne bayan da Arsenal din suka buga wasa 2-2 da  Sporting Lisbon a wani wasa mai matukar kayatarwa na maatakin kungiyoyi 16 a gasar Europa a daren Alhamis.

Dan wasan bayan Faransa, William Saliba ne ya fara ci wa Arsenal kwallo kafin daga bisani Sportin Lisbon su yi amfani da kurakuran masu tsaron baya su saka musu kwallaye biyu ta hannun  Goncalo Inacio da Paulinho.

Advertisements

Dan wasan baya na Sporting Lisbon, dan kasar Japan,  Hidemasa Morita ne ya ci gida, lamarin da ya sa Arsenal suka dawo cikin wasan gabanin haduwa ta 2 da za su yi a Alhamis mai zuwa a filin wasa na Emirates.

Advertisements
Advertisements

Sai dai hakan bai yi wa Arteta dadi ba, duba da yadda tawgarsa ta bari aka saka mata kwallaye 2 a raga a cikin wasa na 2 a jere.

Ya ce  duk inda tawaga ta bari aka saka  mata kwallaye biyu a raga, to lallai ta shiga loko Kenan.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending