Connect with us

News

Hukumar Abinci ta MDD ta ce za ta maido da ayyukanta a Sudan

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

Hukumar Abinci ta majalisar Dinkin Duniya ta ce za ta maido da ayyukanta a Sudan yayin da yaƙi a ƙasar ke yi wa miliyoyin mutane barazanar faɗawa ƙangin yunwa.

 

Advertisement

A wata sanarwa da majalisar Dinkin Duniya ta  fitar ranar Litinin hukumar ta ce tana sa ran fara rabar da abinci a jihohin edaref da Gezira da Kassala da kuma jihar White Nile a cikin kwanaki masu zuwa.

Ba Ruwanmu Da Wasikar Hudu Don Mun Umurce Shi Ya Mika Kansa Ga ‘Yan Sanda – INEC  

“Za mu ɗauki matakai domin tabbatar da kare lafiyar ma’aikatanmu da ƙawayenmu yayin da muƙe ƙoƙarin taimaka miliyoyin mutane da ke cikin tsananin buƙatar taimakon”, kamar yadda sanarwar ta bayyana.

Advertisement

 

Hukumar ta dakatar da ayyukanta a ƙasar ne tun a ranar farko da aka fara yaƙin bayan da aka kashe ma’aikatanta uku.

Advertisement

 

Hukumar Abincin ta Majalisar Dinkin Duniyar ta bayyana cewa mutum miliyan 15 na cikin tsananin buƙatar abinci da rashin tsaro, tun kafin ɓarkewar rikicin.

Advertisement

 

Ta kuma bayyana cewa adadin zai ƙara yayin da ake ci gaba da faɗan.

Advertisement

 

 

Advertisement

Bbc

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending