News
Hukumar Abinci ta MDD ta ce za ta maido da ayyukanta a Sudan
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Hukumar Abinci ta majalisar Dinkin Duniya ta ce za ta maido da ayyukanta a Sudan yayin da yaƙi a ƙasar ke yi wa miliyoyin mutane barazanar faɗawa ƙangin yunwa.
A wata sanarwa da majalisar Dinkin Duniya ta fitar ranar Litinin hukumar ta ce tana sa ran fara rabar da abinci a jihohin edaref da Gezira da Kassala da kuma jihar White Nile a cikin kwanaki masu zuwa.
Ba Ruwanmu Da Wasikar Hudu Don Mun Umurce Shi Ya Mika Kansa Ga ‘Yan Sanda – INEC
“Za mu ɗauki matakai domin tabbatar da kare lafiyar ma’aikatanmu da ƙawayenmu yayin da muƙe ƙoƙarin taimaka miliyoyin mutane da ke cikin tsananin buƙatar taimakon”, kamar yadda sanarwar ta bayyana.
Hukumar ta dakatar da ayyukanta a ƙasar ne tun a ranar farko da aka fara yaƙin bayan da aka kashe ma’aikatanta uku.
Hukumar Abincin ta Majalisar Dinkin Duniyar ta bayyana cewa mutum miliyan 15 na cikin tsananin buƙatar abinci da rashin tsaro, tun kafin ɓarkewar rikicin.
Ta kuma bayyana cewa adadin zai ƙara yayin da ake ci gaba da faɗan.
Bbc
