Connect with us

Business

An samu ƙaruwar hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

 

Hukumar ƙididiga ta Najeriya ta ce hauhawar farashin kayayyaki a ƙasar ya ƙaru zuwa kashi 22.2 cikin ɗari a watan Afirlu.

Advertisement

Rahoton wata-wata da hukumar ke fitarwa ya nuna cewa hauhawar farashin a watan Afrilu ya ƙaru da kashi 0.18 idan aka kwatanta da watan Maris da ya gabace shi.

Hukumar ta ce idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata farashin kayyakin ya ƙaru da kashi 5.40, wanda a watan Afrilun 2022 hauhawar farashin ke kashi 16.82 cikin 100.

Advertisement

Dan jarida, Ndace, ya wallafa littatafai uku kan yadda Buratai yai nasarar yaƙi da Boko Haram/ISWAP

”Abubuwan da farashinsu ya ƙaru sun haɗar da kayan abinci da lemuka wanda farashinsu ya ƙarau da kashi 11.51, sai ruwa da wutar lantarki da iskar gas da man fetur da suka samu ƙarin kashi 3.7, kayan tufafi da takalma su ma farashinsu ya ƙaru da kshi 1.7…”kamar yadda rahoton hukumar ya nuna.

Rahoton ya nuna cewa farashin abinci a watan Afrilu ya kai kashi 24 cikin 100, wato ƙarin kashi 6.24 idan aka kwatantan da watan Afrilun 2022.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending