Connect with us

News

Ana Shirin Jana’izar Wazirin Kano Mai Murabus

Published

on

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADIN

 

Advertisement

 

Jihar Kano na alhinin rasuwar Wazirin Kano murabus, kuma Babban limamin Waje, Sheik Mohammad Nasir Mohammad.

Advertisement

Wani daga cikin makusantan  iyalansa, Sani Abdallah  Wudilawa   ya tabbatar da labarin rasuwar  marigayin ga manema labaraai

Babban malamin ya rasu ne a ranar Laraba 7 ga watan Yuni bayan ya yi fama da jinyar rashin lafiya.

Advertisement

Tirela Ta Kashe Yaro A Wurin Dibar ‘Ganima’ A Kano

Za a gudanar da jana’izarsa yau Alhamis  8 ga watan Yuni a fadar sarkin Kano.

Malamin addinin musuluncin ya rasu yana da shekara 87 a duniya.

Advertisement

A 2014 ne marigayi Ado Bayero ya naɗa Sheikh Nasir sarautar Wazirin Kano naɗin da ya ci karo da turjiya daga gwamnatin jihar Kano ta wancan lokaci.

Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya aike da saƙon ta’aziyyarsa ga iyalan mamacin, ɗalibansa da al’ummar jihar Kano.

Advertisement

Gwamnan ya bayyana marigayin amatsayin fitaccen malamin addinin Musulunci wanda ya bayar da gudunmawa mai yawa wajen cigaban addinin Musulunci ga daukacin al’ummar musulmin duniya.

A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature ya fitar, ta ruwaito gwamnan yana kuma bayyana Sheikh Nasir a matsayin wanda ya yi rayuwa abar koyi.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending