News
Hukumar NAFDAC Ta Gargadi Al’umma Kan Wasu Magunguna Masu ‘Hadari’
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta kasa (NAFDAC), ta ja hankalin jama’a kan yawaitar magungunan ganye na (Herbal) da ba a amince da su ba a fadin kasar nan.
Kayayyakin magungunan wadanda ta bayyana a matsayin “masu hadari”.
Shugaba kasa Bola Ahmad Tinubu Zai Hallarci Taron Kolin Tattalin Arziki a Paris
Babbar darakta na Hukumar ta NAFDAC, Farfesa Mojisola Adeyeye, ta shaida wa manema labarai a Abuja ranar Litinin din nan cewa, galibin magungunan da ake amfani da su na ganye ne na snuff da na liquid, wadanda ta ce barayi ne a tituna ke siyar da su.
Gidan talabijin na Channels ya rawaito cewa Babban daraktan ya kuma lura cewa, tawagar rundunar hukumar sun fara aikin dakile masana’antun da ‘yan kasuwar da ke siyar da irin wadannan kayayyakin da ba a tantance ba.
