Sports
Eden Hazard Ya Yi Ritaya Daga Kwallon Kafa
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Tsohon dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Chelsea, Eden Hazard ya sanar da yin ritaya daga buga kwallo bayan ya bar kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid a karshen kakar wasan da ta gabata.
Hazard, mai shekara 32, ya koma Madrid ne daga Chelsea a shekarar 2019 kan kudi fam miliyan 89, amma ya buga wasanni 54 kawai a gasar La Liga.
Yan asalin jihar Yobe sunyi Bikin cika shekaru dari Biyu da shigowar su Katsina
Ya lashe kofunan gasar Firimiyar Ingila sau biyu a lokacin da yake Stamford Bridge.
“Bayan shekaru 16 da buga wasanni sama da 700, na yanke shawarar kawo karshen sana’ata a matsayin kwararren dan kwallon kafa,” in ji Hazard.
Hazard dai ya fara taka leda a kungiyar Lille ta kasar Faransa inda ya zura kwallaye 50 a wasanni 149 da ya buga sannan kuma ya taimakawa kungiyar ta lashe kofin Ligue 1.
Hazard ya zura kwallaye 110 a wasanni 352 da ya buga wa Chelsea ciki har da wanda ya yi nasara a wasan karshe na gasar Europa ta 2019 da Arsenal a wasansa na karshe a kungiyar.
