Connect with us

News

Dalibin Aji Biyar A Jami’ar ABU Ya Shiga Hannu Kan Zargin Lalata Da Kuma Kisan Wani Mai Shekaru 17

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Wani dalibin aji biyar a Jami’ar Ahmadu Bello dake Zariya (ABU) ya shiga hannu kan zargin lalata da kuma kisan wani dan sakandare mai shekaru 17 a Jihar Bauchi.

Dalibin jami’ar wanda ke karatun a fannin likitancin dabbobi ya fada komar Hukumar Tsaron Farin Kaya (NSCDC) ne bayan an tsinci gawar dan sakandaren a yashe a gefen titin wajen gari a Karamar Hukumar Misali ta Jihar Bauchi.

Wajibi Ne Ma’aikatan Hukumar EFCC Su Bayyana Kadarorinsu – Ola Olukayode

Kwamandan Hukumar Tsaron Farin Kaya na jihar, Ilelaboye Oyejide, ya ce bayan tsintar gawar a yashe cikin farin kyalle, “aka kai ta Babban Asibitin Misau, likitoci suka tabbatar rai ya yi halinsa, sannan aka gawar ga iyayensa suka yi masa jana’iza.

Kwamandan Hukumar ya ce wanda ake zargin ya amsa laifin a yayin da ake masa tambayoyi, kuma a bisa hakan za a gurfanar da shi a kotu.

Oyejide ya bayyana cewa wanda ake zargin ya shaida wa masu bincike cewa dan sakandaren ne zaro wuka ya yiwo kansa da ita, suka yi ta kokawa, inda a garin kare kansa ya soka wa marigayin wukar da ta yi ajalinsa.

Advertisement

A wani labarin kuma Wajibi Ne Ma’aikatan Hukumar EFCC Su Bayyana Kadarorinsu – Ola Olukayode

Gwamnatin tarayya ta ce yanzu haka shirye-shirye sunyi nisa domin sauya akalar motoci har milyan 10 masu amfani da man fetir zuwa amfani da Gas nan da watanni 36 masu zuwa.

Karaminin ministan Mai, Ekperikpe Ekpo ne ya baiyana haka a yayin baje kolin mai da iskar gas na shekarar bana wanda ake gudanarwa a birnin Abu Dhabi na hadaddiyar daular larabawa.

A wata sanarwa da kakakinsa Louis Ibah ya fitar, ya baiyaan cewar a yanzu haka anyi kawance da kanfanoni masu zaman kansu domin kawo kayayyakin da za’a yi amfani dasu wajen sauya akalar motocin nan da watanni 9 masu zuwa.

Ya ce matakin wani yunkuri ne na inganta yin amfani da Gas a tsakanin motocin kasar a maimakon Man fetir da suka dogara dashi.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending