News
Wajibi Ne Ma’aikatan Hukumar EFCC Su Bayyana Kadarorinsu – Ola Olukayode
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Shugaban hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC Ola Olukayode ya umarci daukacin ma’aikatan hukumar su gagauta ayyana kadarorin da suka mallaka bisa tanain tsarin aiki.
Mai Magana da yawun hukumar ta EFCC Dele Oyewale shine ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa, yace shugaban ya bada umarnin a wata ganawa da ma’aikata dake shalkwatar EFCC a Abuja.
Wasu karin mutane biyu sun mutu a hannun ‘yan ta’adda a yankin Birnin-Gwari da ke jihar Kaduna.
Oyewale ya ambato Olukoyede yana cewa dole ne a rayu ta hanyar kafa tsari tare da kyawawan misalai.
A matsayin hukumar dake yaki da cin hanci da rashawa, dole ne hannayen ma’aikata su kasance da tsabta don haka wajibi ne kowa ya bayyana kadarorin da ya mallaka.
Da yake kira ga ma’aikatan hukumar da su mai da hankali sosai kan yadda ake yaki da laifukan tattalin arziki da hada-hadar kudi, Olukoyede ya ce kamata ya yi a mayar da irin wannan kokari wajen bunkasa tattalin arzikin al’umma, da samar da yanayi mai kyau na bunkasa zuba jari da kuma karfafa tushen tattalin arzikin kasa.
A wani labarin kuma Wasu karin mutane biyu sun mutu a hannun ‘yan ta’adda a yankin Birnin-Gwari da ke jihar Kaduna.
Gwamnatin tarayya ta ce yanzu haka shirye-shirye sunyi nisa domin sauya akalar motoci har milyan 10 masu amfani da man fetir zuwa amfani da Gas nan da watanni 36 masu zuwa.
Karaminin ministan Mai, Ekperikpe Ekpo ne ya baiyana haka a yayin baje kolin mai da iskar gas na shekarar bana wanda ake gudanarwa a birnin Abu Dhabi na hadaddiyar daular larabawa.
A wata sanarwa da kakakinsa Louis Ibah ya fitar, ya baiyaan cewar a yanzu haka anyi kawance da kanfanoni masu zaman kansu domin kawo kayayyakin da za’a yi amfani dasu wajen sauya akalar motocin nan da watanni 9 masu zuwa.
Ya ce matakin wani yunkuri ne na inganta yin amfani da Gas a tsakanin motocin kasar a maimakon Man fetir da suka dogara dashi
-
News3 days ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion6 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News2 days ago
Zaben 2027: INEC Ta Amince Da Atiku Abubakar, ‘Yan Takarar ADC 470
