News
Hukumar Kula Da Yanayi Tayi Hasashen Samun Hazo Da Kura A ‘Yan Kwanaki Masu Zuwa
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Hukumar kula da yanayi ta kasa ta baiyana cewar za’a fuskanci karuwar Hazo da kuma ‘kura wanda zai iya haddasa rashin gani sosai a ‘yan kwanaki masu zuwa
Hukumar ta baiyana haka ne ta cikin wata sanarwa mai dauke dasa hannun shugabanta Muntari Yusuf Ibrahim, wadda aka fitar jiya a Abuja.
Majalisar wakilai ta yi watsi da buƙatar Tinubu ta sayen jirgin ruwan shaƙatawa
Ta baiyana cewar za’a fuskanci kadawar iska mai karfi da tashin kura a wasu bangarori na kasar nan musamman jihohin katsina da kano da Nguru da jigawa da Fotiskuma da kuma Maiduguri nan da sa’oi 24 masu zuwa.
Daga nan sanarwar ta bukaci jama’a dasu daukin matakan kula da lafiyarsu da kuma yin tuki cikin natsuwa ga masu ababen hawa.
A wani labarin kuma Majalisar wakilai ta yi watsi da buƙatar Tinubu ta sayen jirgin ruwan shaƙatawa
Gwamnatin tarayya ta ce yanzu haka shirye-shirye sunyi nisa domin sauya akalar motoci har milyan 10 masu amfani da man fetir zuwa amfani da Gas nan da watanni 36 masu zuwa.
Karaminin ministan Mai, Ekperikpe Ekpo ne ya baiyana haka a yayin baje kolin mai da iskar gas na shekarar bana wanda ake gudanarwa a birnin Abu Dhabi na hadaddiyar daular larabawa.
A wata sanarwa da kakakinsa Louis Ibah ya fitar, ya baiyaan cewar a yanzu haka anyi kawance da kanfanoni masu zaman kansu domin kawo kayayyakin da za’a yi amfani dasu wajen sauya akalar motocin nan da watanni 9 masu zuwa.
Ya ce matakin wani yunkuri ne na inganta yin amfani da Gas a tsakanin motocin kasar a maimakon Man fetir da suka dogara dashi.
