Connect with us

News

CBN Ya Tsawaita Wa’adin Amfani da Tsofaffin Takardun Naira Sai Baba Tagani

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

 

Babban Bankin Najeriya ya ce tsoffin takardun naira da aka sake wa fasali, za su ci gaba da zama halastattun kudi har bayan wa’adin farko da hukumomin kasar suka sanya na 31 ga watan Disamban 2023.

Ya ce an dauki matakin ne bisa dacewa da tsarin hada-hadar kudi na kasashen duniya da kuma hana sake maimaita abin da ya faru a baya.

Zargin Al mundahanar N109bn: Kotu ta soke belin tsohon Akanta-Janar na Tarayya 

Wata sanarwa da daraktan sadarwa na Babban Bankin, Isa AbdulMumin ya fitar, ta ce CBN yana aiki da hukumomin da ke da jibi don ganin an soke hukuncin kotu da ya ba da umarni kan karewar wa’adin takardun kudin.

 

Advertisement

Babban Bankin ya ce yana sanar da al’ummar kasar game da kudurinsa na kara wa’adin tsoffin takardun da ake sake na naira 200 da 500 da kuma 1000 har zuwa abin da hali ya yi.

 

Ya kuma umarci dukkan rassansa a fadin Najeriya su ci gaba da bayarwa da kuma karbar duk takardun kudin Najeriya, tsofaffi da kuma sababbin da ake sake fasalinsu.

 

Haka zalika ya yi kira ga al’ummar kasar su ma su ci gaba da karbar dukkan takardun tsoffi da sabbin naira don hada-hadar kudi ta yau da kullum.

 

Advertisement

A watan Oktoban 2022 ne, Babban Bankin Najeriyar ya bullo da tsarin sake fasalin takardar naira 200 da 500 da 1000, kuma ya ba da wa’adin dakatar da karbar tsoffin takardun da aka sauya, a matsayin halastattun kudi.

 

Sai dai takaddama ta ɓarke, inda wasu gwamnonin jihohi suka shigar da kara gaban kotu, wadda ta bai wa gwamnatin tarayya da babban bankin kasar rashin gaskiya, sannan ta umarci a ci gaba da amfani da tsoffin takardun nairar har zuwa karshen watan Disamban bana.

 

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending