Connect with us

News

Korarrun ‘Yan Jam’iyya Ne Masu Nuna Rashin Amincewa Da Abba Da Kwankwaso  -Jam’iyyar NNPP

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

 

Advertisement

Jam’iyyar NNPP ta nesanta kanta da wasu dake Ikirarin ‘ya’yan jam’iyyar ne suna kalaman rashin amincewa da jagoran jam’iyyar na kasa, Rabi’u Musa Kwankwaso da gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf.

Kwamitin gudanarwa na jam’iyyar na kasa a karkashin jagorancin mukaddashin shugabanta na kasa, Abba Kawu Ali, wanda ya yi magana ta bakin mai magana da yawun jam’iyyar, Ladipo Johnson, ya ce an dade da korar wadanda suke kiran kan nasu amatsayin ‘ya’yan jam’iyyar ta NNPP.

Advertisement

Bayan Zanga-Zangar Dalibai Jami’ar ATBU ta Rufe Harabar makarantar

A ranar Litinin dai Dr Agbo Major a Abuja ya shaidawa manema labarai cewa kotun karrakin zabe da kotun daukaka kara sun yanke hukuncin cewa gwamnan jihar Kano ba mamban jam’iyyar NNPP ba saboda rashin bin kundin tsarin mulkin jam’iyyar.

Amma a cikin wani martani na gaggawa, Johnson ya bayyana ikirarin amatsayin Tuggu daga korarrun mambobin NNPP, kuma farfaganda.

Advertisement

Ya kara da cewa an dauki nauyinsu ne domin kawo rashin jituwa a cikin jam’iyyar.

A wani labarin kuma Bayan Zanga-Zangar Dalibai Jami’ar ATBU ta Rufe Harabar makarantar

Advertisement

Shaidu da kuma ‘yan jaridar Gaza na ba da rahoton ganin tankokin yaƙin Isra’ila da motoci masu silke a kusa da unguwar Khan Younis da ke Zrin Gaza.

Sun ce sun doshi gabas zuwa yankunan Abasan, da Khuzaa, waɗanda ke kusa da katangar iyaka tsakanin Isra’la da Gaza.

Advertisement

Tuni sojojin Isra’ila suka jejjefa takardun sanarwa ga Falasɗinawan da ke kudanci, suna umartar su da su koma wasu yankunan.

Mai magana da yawun rundunar, Daniel Hagari, ya ce duk inda mayaƙan Hamas suka shiga su ma sai sun shiga.

Advertisement

Tun bayan ci gaba da yaƙin, Isra’ila ta ƙara yawa da kuma faɗaɗa hare-haren da take kaiwa zuwa kudancin zirin.

Akasarin Falasɗinawan da aka kashe a baya-bayan nan sun koma can ne daga wasu wuraren na Gaza.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending