News
Bayan Zanga-Zangar Dalibai Jami’ar ATBU ta Rufe Harabar makarantar
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Hukumomin Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa da ke Yelwa a jihar Bauchi sun rufe makarantar sakamakon zanga-zangar da dalibai suka yi kan kisan da aka yi wa wani dalibi
Manufar Garkame Jami’ar shi ne hana tabarbarewar doka da oda yayin da ake zargin wasu ‘yan daba ne suka sace zanga-zangar
KANO: Hukumar Kwastam ta ce ta samu Naira biliyan 6.9 a matsayin kudaden shiga a watan Nuwamba,
An umurci dukkan daliban makarantun biyu da su fice daga harabar jami’ar ba tare da bata lokaci ba, saboda rashin bin umarnin na iya haifar da hukuncin da ya dace daga hukumar
Hukumomin Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa da ke Yelwa a jihar Bauchi sun rufe makarantar sakamakon zanga-zangar da dalibai suka yi kan kisan da aka yi wa Joseph Agabaidu, dalibin sashen nazarin kasa na shekarar karshe, a wani yunkurin fashi da makami kamar yanda Jaridar Daily Post ta ruwaito
A cikin wata takarda da aka fitar wadda mataimakiyar rijistarar ta sanya wa hannu, Haj. Fatima Inuwa Abdullahi,tace hukumar gudanarwar jami’ar ta amince da rufe jami’ar na tsawon mako guda daga ranar Litinin 4 ga watan Disamba zuwa Lahadi 10 ga watan Disamba.
A cewar takardar, manufar ita ce hana tabarbarewar doka da oda yayin da ake zargin wasu ‘yan daba ne suka sace zanga-zangar.
A wani bangare na sanarwar na cewa: “Kamar yadda za ku iya tunawa, an yi zargin kashe Joseph Aga Baidu, dalibi mai matakin aji 500 na sashen nazarin kasa kwanan nan a Yelwa Kagadama, wanda ya sanya wasu bata gari suka gudanar da zanga-zanga a kewayen harabar Yelwa, wanda hakan ya kawo cikas ga zaman lafiya.
“Saboda abubuwan da suka gabata, Mataimakin Shugaban Jami’ar, a madadin Majalisar Dattawa, ya amince da rufe jami’ar na tsawon mako guda daga ranar Litinin 4 zuwa Lahadi 10 ga watan Disamba, 2023.
“Saboda haka, an umurce ni da in nemi dukkan daliban da suka kammala karatun digiri na biyu a makarantun biyu da su fice daga harabar jami’ar ba tare da bata lokaci ba, saboda rashin bin umarnin na iya haifar da hukuncin da ya dace daga hukumar.”
Jaridar Inda Ranka ta rawaito cewa an samu tashin hankali ne a ranar Litinin a jami’ar yayin da jami’an rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi suka jefawa daliban da suka yi zanga-zangar lumana hayaki Mai sa hawaye.
Lamarin ya faru ne a ranar Asabar da daddare, inda aka kai wa dalibin makarantar sashin nazarin kasa mai mataki aji 500 da aka ce yana komawa masaukinsa da ke kusa da kasuwar Yelwan Tudu da ke unguwar Yelwa, a wajen babban birnin Bauchi, da misalin karfe 7 na dare.
Rahotanni sun bayyana cewa wanda aka kashe din ya mutu ne sakamakon raunin da ya samu.
Sakamakon haka, zanga-zangar da daliban suka shirya ta kama ‘yan sanda, inda suka ajiye motocinsu masu sulke daura da kofar shiga makarantar a ranar Litinin.
Lamarin dai ya ta’azzara ne yayin da daliban suka rufe kofar, inda suka kawo cikas ga harkokin Ilimi a harabar jami’ar, yayin da yunkurin kwantar da hankulan su ya ci karo da wakokin hadin kai.
