Connect with us

News

Yan Nijeriya Na Shan Bakar Wahala Saboda Rashin Iya Mulki -Obi

Published

on

Dan takarar jam’iyyar Labour Party, LP, a zaben shugaban kasa, Peter Obi

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Dan takarar jam’iyyar Labour Party, LP, a zaben shugaban kasa, Peter Obi, a ranar Litinin ya koka da cewa ‘yan Najeriya na cikin mawuyacin hali saboda munanan manufofin gwamnati.

Advertisement

Daily Post ta ruwaito cewa Obi ya ce duk da wahalhalun da ake ciki, dole ‘yan Najeriya su yi hakuri da halin da suka tsincin kansu na rashin iya shugabancin shugabanninsu.

Muna Da Yakinin Kotun Koli Za Ta Yi Mana Adalci – Gwamnan Kano

Ya bayyana hakan ne a sakonsa na Kirsimeti ga ‘yan Najeriya ta hanyar wasu sakonni da ya wallafa a shafinsa na Twitter.

Advertisement

Wahalhalun da ake fama da su a kasar nan, illar cizon sauro na munanan manufofin gwamnati da kuma rashin shugabanci nagari sun dakushe fatan yawancin ‘yan Najeriya.

Masifu da kalubalen da muke fuskanta a wannan lokaci bai kamata su hana mu fahimtar ainihin halittarmu da kuma muhimmancin neman rahamar Ubangiji a kowane lokaci ba.

Advertisement

Bugu da kari, koma bayan da muke fuskanta a halin yanzu bai kamata ya hana mu a matsayinmu na al’umma masu burin shawo kan matsalolin da muke ciki ba, da kuma sanin cikakken ƙarfin ƙasarmu mai albarka.

Don haka ina yi muku wasiyya da ku yi amfani da wannan gagarumin buki wajen gabatar da addu’o’i na musamman ga Allah domin kasarmu ta yadda za mu samu damar hada kan sauran al’ummar duniya.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending