News
Muna Da Yakinin Kotun Koli Za Ta Yi Mana Adalci – Gwamnan Kano
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Yayin da al’ummar jihar Kano ke jiran hukuncin kotun koli a kan karar da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya shigar, ya bukaci mazauna jihar da su amince da alkalan kotun koli.
Gwamnan ya kuma yabawa alkalan bisa jajircewarsu wajen tabbatar da gaskiya da adalci wajen gudanar da shari’o’in da ke gabansu.
Gwamnan ya bayyana haka ne a lokacin da yake kaddamar da horas da matasa 2500 kan harkar tsaro a jihar a filin wasa na Sani Abacha, ranar Lahadi.
“Ina so in yi amfani da wannan dama domin yaba wa alkalan kotun koli bisa jajircewarsu wajen tabbatar da gaskiya da adalci.
“Zan kuma so in yi kira ga mutane da su amince da su kuma su ci gaba da mutunta amincin su,” in ji Yusuf.
Ya kuma tabbatar wa magoya bayan sa cewa zai yi nasara a karar da ya shigar a kotun koli kan hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke wanda ya tabbatar da hukuncin kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan jihar Kano da ta soke zabensa.
Ya ce taron na daga cikin tsare-tsaren gwamnatin sa na ganin an samar da ayyukan yi ga matasan jihar da suka hada kai.
Ya ci gaba da cewa kaddamar da horon a makarantar horar da jami’an tsaro zai fara ne da wani sabon tsarin tsaro da aka bullo da shi.
Wadanda suka ci gajiyar shirin sun fito ne daga kananan hukumomi 44 na jihar, kuma bayan kammala horon za a samar musu da ayyukan yi a Ma’aikatu na Jiha, da kuma kananan hukumomi.
