News
Hukumar Yan Sanda Ta Karyata Batun Karbar Naira 2,000 Daga Hannun Masu Neman Aikin
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Hukumar kula da ayyukan ‘yan sanda, PSC, ta yi watsi da maganar da ake yi na cewa tana neman biyan Naira dubu biyu daga hannun masu sha’awar shiga aikin yan sanda.
A cikin wata sanarwa da shugaban hulda da jama’a Ikechukwu Ani ya fitar, ya ce sakon da ke dauke da sunan hukumar a sama wanda ke cewa duk wanda zai zo domin gudanar da aikin tantancewa a hukumar yazo da Naira 2,000 karya ce tsagwaronta.
Mutum 4 Sun Mutu, 59 Sun Jikkata A Hatsarin Mota A Hanyar Kaduna zuwa Abuja
A cewar sanarwar,hankalin hukumar ‘yan sanda ya tafi kan wani labari na karya a kafafen sada zumunta na yanar gizo na neman wadanda ke son tantancewa domin daukar ma’aikatan ‘yan sandan Najeriya da su zo da kudi N2000.
Jaridar The Nation ta ruwaito cewa Don haka Hukumar ta ce tana son yin watsi da wannan magana da kuma raba kan ta daga wannan labarin da aka ce na kage ne da yaudara.
Hukumar a baya a cikin wata sanarwa da ta fitar ta bayyana cewa daukar ma’aikata gaba daya daga matakin rajista zuwa mataki na karshe wanda shine gwajin lafiya kuma tana son bayyana cewa babu wani abu da ya canza.
A wani labarin kuma Mutum 4 Sun Mutu, 59 Sun Jikkata A Hatsarin Mota A Hanyar Kaduna zuwa Abuja
Babban Bankin Najeriya CBN ya sauya matsayarsa kan hada-hada da kuɗin intanet ko kuma cryptocurrency a ƙasar.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito wata sanarwa da bankin ya fitar ranar Juma’a da ke umartar bankunan kasuwanci na Najeriya cewa su yi watsi da haramcin da ya saka kan amfani da kuɗin na crypto tu a 2021.
CBN ya ce yadda ake yayin kuɗin na crypto yanzu a faɗin duniya ya nuna irin buƙatar da ake da ita ta saka dokoki a kan sa.
“A watan Fabarairun 2021 CBN ya haramta wa bankuna da sauran cibiyoyin kuɗi amfani da cryptocurrency saboda almundahanar kuɗi da kuma ɗaukar nauyin ta’addanci,” in ji sanarwar.
“Sai dai kuma, abin da ke faruwa a duniya ya nuna cewa akwai buƙatar a kula da dukiyoyin hada-hada ta intanet wato Virtual Assets Service Providers (V/ASPs).”
Ya ƙara da cewa hukumar kula da hada-hada da hannayen jari za ta fitar dokoki da sharuɗɗan amfani da dukiyoyoin intanet ɗin.
Amma babban bankin ya jaddada haramcin yin kasuwanci, ko kuma mallakar asusun crypto ga bankunan kasuwancin su da kansu
-
News3 days ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion7 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News3 days ago
Zaben 2027: INEC Ta Amince Da Atiku Abubakar, ‘Yan Takarar ADC 470
