Connect with us

News

Shugaba Tinubu ya kasa cika alkawuran da ta yi wa ma’aikata a 2023. – NLC

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Kungiyar Kwadago ta Najeriya NLC, ta ce gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta yi rashin aminci a kan alkawuran da ta yi wa ma’aikata a 2023.

A wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi, shugaban kungiyar ta NLC, Joe Ajaero, ya caccaki gwamnatin tarayya kan rashin kiyaye yarjejeniya da ma’aikatan Najeriya duk da hakurin da kungiyoyin kwadago suka nuna.

Yan bindiga sun kashe wasu mutane a Nijar

Ajaero ya lura cewa mambobin kungiyar “sun fuskanci rashin tabbas, kuma sun shaida lokutan da watakila ya sa su cikin damuwa.”

Sanarwa ta kara da cewa gwamnati ta kasa cika abin da ake tsammani na alkawarin biyan N35,000 na wucin gadi na tsawon watanni uku, da kammala aikin matatar mai na Fatakwal, da aiwatar da shirin  iskar gas.

 

Advertisement

“Ba a aiwatar da kyautar albashin N35,000 da aminci ba; matatar mai ta Port Harcourt PH ba ta zo aiki ba kamar yadda aka yi hasashe yayin da ba a kaddamar da majalisar tattaunawa kan mafi karancin albashi na kasa ba kamar yadda aka amince; wakilan gwamnati sun gurbata aikin damtse iskar gas na CNG don amfanin wasu kadan,” inji shi.

DAILY POST ta ruwaito cewa kungiyoyin kwadagon da suka hada da NLC da Trade Union Congress, TUC, sun shelanta yajin aikin a fadin kasar saboda cire tallafin mai a watan Satumba.

A wani labarin kuma Yan bindiga sun kashe wasu mutane a Nijar

Babban Bankin Najeriya CBN ya sauya matsayarsa kan hada-hada da kuɗin intanet ko kuma cryptocurrency a ƙasar.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito wata sanarwa da bankin ya fitar ranar Juma’a da ke umartar bankunan kasuwanci na Najeriya cewa su yi watsi da haramcin da ya saka kan amfani da kuɗin na crypto tu a 2021.

CBN ya ce yadda ake yayin kuɗin na crypto yanzu a faɗin duniya ya nuna irin buƙatar da ake da ita ta saka dokoki a kan sa.

Advertisement

“A watan Fabarairun 2021 CBN ya haramta wa bankuna da sauran cibiyoyin kuɗi amfani da cryptocurrency saboda almundahanar kuɗi da kuma ɗaukar nauyin ta’addanci,” in ji sanarwar.

“Sai dai kuma, abin da ke faruwa a duniya ya nuna cewa akwai buƙatar a kula da dukiyoyin hada-hada ta intanet wato Virtual Assets Service Providers (V/ASPs).”

Ya ƙara da cewa hukumar kula da hada-hada da hannayen jari za ta fitar dokoki da sharuɗɗan amfani da dukiyoyoin intanet ɗin.

Amma babban bankin ya jaddada haramcin yin kasuwanci, ko kuma mallakar asusun crypto ga bankunan kasuwancin su da kansu

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending