Connect with us

News

Yan-sanda a jihar Yobe sun An kama Malamin Jami’ar  bisa zargin kashe matarsa

Published

on

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN

 

Advertisement

Rundunar ‘yan-sandan Nigeria reshen jihar Yobe ta kama wani malamin Jami’a mai suna Abubakar Musa sakamakon kisan gilla da aka yi wa mai dakinsa.

Abubakar Musa da matar ta sa mai suna Ammi Mamman dukkanninsu malamai ne a sashen nazarin kimiyyar siyasa da ke Jami’ar jihar Yobe.

Advertisement

Har Yanzu Gas Din Girki Na Gagarar Talakan Najeriya Bayan Wata Daya Da Alkawarin Gwamnati

Mai magana da yawun rundunar DSP Dungus Abdukkarim shine ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar da safiyar juma’a a birnin Damaturu.

A cewar-sa, wannan mummunan al’amari ya faru ne da misalin karfe 4 da mintuna 48 na daren Alhamis a gidansu da ke rukunin gidaje na Bra-Bra da ke Damaturu.

Advertisement

DSP Dungus Abdulkarim ya ce, tun farko an kira ‘yan-sanda an sanar da su cewa, an kashe wata mata a wani gida da ke unguwar ta Bra-Bra.

Ya ce, bayan isar ‘yan-sanda wajen da lamarin ya faru ne sai su ka samu marigayiya Ammi Mamman kwance shame-shame cikin jini, da alamar an caka mata wani abu mai kaifi a wuyarta, wanda wannan ne ya yi sanadiyar mutuwarta.

Advertisement

Mai magana da yawun rundunar ‘yan-sandan na jihar Yobe ya ce, an kama mijin marigayiyar ne saboda yana tare da ita suna kwance akan gado lokacin da lamarin ya faru.

Sai dai ya ce, tuni sashen bincike na rundunra ya yi nisa wajen bincike domin yadda kisan ya faru.

Advertisement

A Wani labarin kuma Har Yanzu Gas Din Girki Na Gagarar Talakan Najeriya Bayan Wata Daya Da Alkawarin Gwamnati

Babban Bankin Najeriya CBN ya sauya matsayarsa kan hada-hada da kuɗin intanet ko kuma cryptocurrency a ƙasar.

Advertisement

Jaridar Daily Trust ta ruwaito wata sanarwa da bankin ya fitar ranar Juma’a da ke umartar bankunan kasuwanci na Najeriya cewa su yi watsi da haramcin da ya saka kan amfani da kuɗin na crypto tu a 2021.

CBN ya ce yadda ake yayin kuɗin na crypto yanzu a faɗin duniya ya nuna irin buƙatar da ake da ita ta saka dokoki a kan sa.

Advertisement

“A watan Fabarairun 2021 CBN ya haramta wa bankuna da sauran cibiyoyin kuɗi amfani da cryptocurrency saboda almundahanar kuɗi da kuma ɗaukar nauyin ta’addanci,” in ji sanarwar.

“Sai dai kuma, abin da ke faruwa a duniya ya nuna cewa akwai buƙatar a kula da dukiyoyin hada-hada ta intanet wato Virtual Assets Service Providers (V/ASPs).”

Advertisement

Ya ƙara da cewa hukumar kula da hada-hada da hannayen jari za ta fitar dokoki da sharuɗɗan amfani da dukiyoyoin intanet ɗin.

Amma babban bankin ya jaddada haramcin yin kasuwanci, ko kuma mallakar asusun crypto ga bankunan kasuwancin su da kansu

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending