News
Gwamnatin Taraya Ta Saki Kudi Naira Bilyan 50 Domin Kammala Wasu Ayyuka A Abuja
DAGA SALIM BELLO SALE
Ministan babban Birnin Tarayya Abuja Nyesom Wike, yace gwamnatin taraya ta saki kudi Naira Bilyan 50 daga cikin kwarkwayar kasafin kudin babban Birnin tarayya Abuja domin kammala wasu ayyuka da ake gudanarwa yanzu haka.
Ministan ya bayyana haka ne a jiya, yayin duba wasu ayyuka a babban Birnin tarayya Abuja.
Ya bayyana shirin ma’aikatar sa na hada kai da hukumomin tsaro domin saka Kamarori a babban Birnin tarayya domin tabbatar da tsaro. A karshen shekarar 2023 ne, hadakar majalisar dokokin tarayya ta amince da kudi naira bilyan 61. Da miliyan 555 a matsayin kwarkwaryar kasafin kudin babban Birnin tarayya Abuja.
A wani labarin kuma Tallafin Naira miliyan 200 : Ba Gaskiya Ba ne, Har Yau Ko Mudun Shinkafa Ba A Raba Mana Ba – Sanatoci
Babban Bankin Najeriya CBN ya sauya matsayarsa kan hada-hada da kuɗin intanet ko kuma cryptocurrency a ƙasar.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito wata sanarwa da bankin ya fitar ranar Juma’a da ke umartar bankunan kasuwanci na Najeriya cewa su yi watsi da haramcin da ya saka kan amfani da kuɗin na crypto tu a 2021.
CBN ya ce yadda ake yayin kuɗin na crypto yanzu a faɗin duniya ya nuna irin buƙatar da ake da ita ta saka dokoki a kan sa.
“A watan Fabarairun 2021 CBN ya haramta wa bankuna da sauran cibiyoyin kuɗi amfani da cryptocurrency saboda almundahanar kuɗi da kuma ɗaukar nauyin ta’addanci,” in ji sanarwar.
“Sai dai kuma, abin da ke faruwa a duniya ya nuna cewa akwai buƙatar a kula da dukiyoyin hada-hada ta intanet wato Virtual Assets Service Providers (V/ASPs).”
Ya ƙara da cewa hukumar kula da hada-hada da hannayen jari za ta fitar dokoki da sharuɗɗan amfani da dukiyoyoin intanet ɗin.
Amma babban bankin ya jaddada haramcin yin kasuwanci, ko kuma mallakar asusun crypto ga bankunan kasuwancin su da kansu
