News
Kananan Kamfanoni Miliyan 10 Suka Durkushe A Shekarar 2023 – ASBON
DAGA MARYAM HAMISU SANDA
Kungiyar masu Kananan Masana’antu ta Nijeriya (ASBON) ta bayyana cewa, fiye da kananan masana’antu miliyan 10 ne suka durkushe a shekarar da ta gabata 2023.
Shugaban kungiyar, Femi Egbesola, ya sanar da haka a tattunawarsa da manema labarai, ya ce, kamfanonin sun durkushe ne sakamakon matsalar tattalin arziki a Nijeriya.
Majalisar dokokin jihar Legas ta amince da kasafin kudin shekarar 2024 na naira tiriliyan 2.267
Hukumar kididdiga ta kasa NBC ta bayyana cewa a watan Nuwamba na 2023 an samu hauhawar farashi na kashi 28.20 ba kamar yadda yake ba a watan Oktoba 2023 na kashi 27.33.
Da yake tsokaci a kan yadda matsin tattalin arzikki ya shafi mambobinsu, Egbesola ya bayyana cewa, “Kashi 25 na kamfanonin da ake da su suka mutu a shekarar 2023, wannan ne mafi yawa a tarihin mutuwar kamfanoni a kasar nan.
“A halin yanzu muna da kamfanoni miliyan 40 a kasar nan da bayanan su ke cikin kundin tattara bayanai, idan ka cire kashi 25, yana nuna kenan kamfanoni miliyan 10 suka mutu.
“A wasu kasashen in har aka samu irin haka, gwamnati na sanya dokar ta-baci ne a sashin don wadannan kanana kamfanoni sune ke rikida su zama manyan kamfanoni a nan gaba. Idan zaka kuma yi tambaya a cikin shekara 10 da suka wuce kananan kamfanoni nawa ne suka zama manyan kamfanoni? Lallai ba a abin a zo a gani ba ne”
Ya kuma kara da cewa, in har ana son ceto kananan kamfanoni daga durkushewa a cikin wannan sabuwar shekarar dole gwamnati ta tabbatar da gyara hanyoyi da kuma samar da wutar lantarki da kuma samar da bashi mara ruwa ga kananan kamfanoni don tabbatar da bunkasar su.
In har aka samar da wadannan tabbas kamfanoni da dama za su bunkasa, su kuma taimaka wajen daukar matasanmu aikin yi abin da kuma zai rage ayyuykan masu aikata laifukka a fadin tarayyar Nijeriya.
A wani labarin kuma Majalisar dokokin jihar Legas ta amince da kasafin kudin shekarar 2024 na naira tiriliyan 2.267
Babban Bankin Najeriya CBN ya sauya matsayarsa kan hada-hada da kuɗin intanet ko kuma cryptocurrency a ƙasar.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito wata sanarwa da bankin ya fitar ranar Juma’a da ke umartar bankunan kasuwanci na Najeriya cewa su yi watsi da haramcin da ya saka kan amfani da kuɗin na crypto tu a 2021.
CBN ya ce yadda ake yayin kuɗin na crypto yanzu a faɗin duniya ya nuna irin buƙatar da ake da ita ta saka dokoki a kan sa.
“A watan Fabarairun 2021 CBN ya haramta wa bankuna da sauran cibiyoyin kuɗi amfani da cryptocurrency saboda almundahanar kuɗi da kuma ɗaukar nauyin ta’addanci,” in ji sanarwar.
“Sai dai kuma, abin da ke faruwa a duniya ya nuna cewa akwai buƙatar a kula da dukiyoyin hada-hada ta intanet wato Virtual Assets Service Providers (V/ASPs).”
Ya ƙara da cewa hukumar kula da hada-hada da hannayen jari za ta fitar dokoki da sharuɗɗan amfani da dukiyoyoin intanet ɗin.
Amma babban bankin ya jaddada haramcin yin kasuwanci, ko kuma mallakar asusun crypto ga bankunan kasuwancin su da kansu
