News
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Katsina ta kama wani mutum da buhu 45 na kayan maye.
DAGA MUHAMMAD BASHIR MUSA
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Katsina ta kama wani mutum da buhu 45 na kayan maye.
Kakakin rundunar, ASP Abubakar Sadiq-Aliyu, ne ya bayyana cewa an kama wanda ake zargin mai shekarua 30 ne a Malumfashi.
Kotun sojojin Jamhuriyar Nijar ta bayar da umarni a saki dan Bazoum
A cewarsa, abubuwan da aka kwato daga hannun wanda ake zargin sun hada da kwalabe 500 na magungunan maye da wasu allursi.
“A ranar 3 ga watan Janairu, 2024, bisa sahihan bayanan sirri da muka samu daga wata majiya mai tushe, rundunar ta yi nasarar kama wanda ake zargin a Malumfashi.” in ji jami’in.
Ya kara da cewa a yayin binciken wanda ake zargin an kai ga gano wasu haramtattun miyagun kwayoyi.
Kakakin ya bayyana cewa wanda ake zargin wanda dillalin kwayoyi ne, ya tabbatar da mallakar buhu 45 na miyagun kwayoyin.
Aminiya ta ruwaito cewa Sadiq-Aliyu ya bayyana cewa yayin bincike an gano wasu mutum biyu da ke taimaka masa wajen safarar miyagun kwayoyin.
“A halin yanzu, za a mika wanda ake zargi ga hukumar NDLEA don ci gaba da bincike,” in ji shi.
A wani labarin kuma Kotun sojojin Jamhuriyar Nijar ta bayar da umarni a saki dan Bazoum
Babban Bankin Najeriya CBN ya sauya matsayarsa kan hada-hada da kuɗin intanet ko kuma cryptocurrency a ƙasar.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito wata sanarwa da bankin ya fitar ranar Juma’a da ke umartar bankunan kasuwanci na Najeriya cewa su yi watsi da haramcin da ya saka kan amfani da kuɗin na crypto tu a 2021.
CBN ya ce yadda ake yayin kuɗin na crypto yanzu a faɗin duniya ya nuna irin buƙatar da ake da ita ta saka dokoki a kan sa.
“A watan Fabarairun 2021 CBN ya haramta wa bankuna da sauran cibiyoyin kuɗi amfani da cryptocurrency saboda almundahanar kuɗi da kuma ɗaukar nauyin ta’addanci,” in ji sanarwar.
“Sai dai kuma, abin da ke faruwa a duniya ya nuna cewa akwai buƙatar a kula da dukiyoyin hada-hada ta intanet wato Virtual Assets Service Providers (V/ASPs).”
Ya ƙara da cewa hukumar kula da hada-hada da hannayen jari za ta fitar dokoki da sharuɗɗan amfani da dukiyoyoin intanet ɗin.
Amma babban bankin ya jaddada haramcin yin kasuwanci, ko kuma mallakar asusun crypto ga bankunan kasuwancin su da kansu
