Connect with us

News

Mataimakin Gwamnan Jihar Nasarawa Ya Ziyarci Wace Aka Sacewa Jariri Awa 3 Da Haihuwarsa A Asibiti

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN

 

Advertisement

Mataimakin gwamnan jihar Nasarawa Dakta Emmanuel Akabe ya ziyarci Wasila Suleiman yau a asibitin kwararru na Dalhatu Araf Lafia

Ya kuma ba da tabbacin gwamnatin ta jihar Nasarawa a shirye take ta tabbatar da cewa jaririyar ta dawo mata cikin gaggawa.

Advertisement

Ana zargin ma’aikacin bankin UBA ya saci N3,390,000 daga asusun kwastoma a jihar Kano.

Jaridar Inda Ranka ta ruwaito cewa Wata mata ta sace jariri awa uku bayan haihuwarsa a Asibitin Kwararru na Dalhatu Arafat (DASH) da ke garin Lafia, Jihar Nasarawa.

Ana zargin bakuwar ta sace jaririn ne da hadin bakin ’yar uwar mai jegon sa’o’i kadan da haihuwarsa ta hanyar yi wa mahifiyarsa tiyata.

Advertisement

Rahotanni na nuni da cewa bayan haihuwarsa da misalin karfe 3 na asubahin ranar Talata ne jami’an asibiti suka mika jaririn da mai jegon ga wata ’yar uwarta domin ta ci gaba da kula da su.

Wani ganau da ya nemi a boye sunasa ya ce, bayan sun dawo dakin masu jego ne ’yar uwar mai jegon ta kawo mata da wata bakuwa, wadda ake zargin sun hada baki wajen sace jaririn.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending