Labarai
Yadda Aka Kama Sojan Da Ke Kai Wa Bello Turji Kayan Yaki

’Yan sanda sun kama wani korarren soja da ke bai wa jagoran ’yan bindigan Jihar Zamfara, Bello Turji da yaransa kayan sojoji.
Korarren jami’in Sojan Saman Najeriyan mai suna Ahmed Mohammed, ya kasance yana samar da wa ’yan bindiga kakin sojoji na yaki da sauran kayan aikin jami’an tsaro, kafin dubunsa ta cika.
Tsadar Rayuwa: Kasuwancin Awara Ya Bunƙasa A Sanadiyyar Ɓarkewar Yunwa A Kano
Aminiya ta gano cewa Ahmed ya yi aikin sojan sam kawai na tsawon shekaru biyar kafin a kore shi saboda wani laifin da ba a bayyana ba.
Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Najeriya, Muyiwa Adejobi, ya bayyana cewa, an cafke korarrren sojan ne tare da wani abokinsa a hanyarsu ta kai kayan jami’an tsaro da suka dauko daga Kaduna za su kai wani sansanin ’yan bindiga da ke Karamar Hukumar Shinkafi a Jihar Zamfara.
Adejobi ya ce Ahmed ne ya yi wa wani abokin nasa mai suna Mushiri Abubakar, tayin sayar wa ’yan bindiga da kayan da sojoji.
A cewarsa, Mushiri Abubakar ya samar wa sansanonin ’yan ta’adda daban-daban kayan sojoji bayan wadanda ake zargin sun bai wa Bello Turji da tawagarsa.
Da yake gabatar da su a hedikwatar rundunar da ke Abuja, Adejobi ya ce kayayyakin da aka kwato daga hannun wadanda ake zargin sun hada da kakin sojoji guda 10, da huluna da rigunan sanyi dai dai saurans
-
Labarai6 days ago
Gwamnatin Tarayya Za Ta Fara Yi Wa Masu Digirin Ƙasashen Waje Jarrabawa
-
Labarai3 days ago
Jami’an Tsaro A Pakistan Sun Kama ’Yan Najeriya 20 Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi
-
Labarai2 days ago
Hare-haren Ta’addanci Ya Yi Sanadiyyar Mutuwar Mutum 835 A Najeriya Cikin Wata Guda – Rahoto
