News
Wani Zaki Ya Kashe Mutumin Da Ya Yi Shekara Tara Yana Renonsa A Jami’ar Obafemi Awolowo (Oau) Da Ke Jihar Osun.
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Wani zaki ya kashe mutumin da ya yi shekara tara yana renonsa a Jami’ar Obafemi Awolowo (OAU) da ke Jihar Osun.
Mai magana da yawun jami’ar, Abiodun Olarewaju, ya ce lamarin ya faru ne a ranar Litinin kuma a daidai lokacin da marigayin ke ƙoƙarin bai wa zakin da sauran ‘yan uwansa abinci kamar yadda ya saba.
Ƙungiyar Direbobin Tankokin Dakon Man Fetur Sun Fara Yajin Aikin Akan Tsadar Rayuwa
An ce marigayin shi ne jami’in da ke kula da lafiyar dabbobin da ke ajiye a sashen ajiye dabbobi na jami’ar, inda ya shafe shekara tara yana kula da matashin zaƙin da ya yi ajalinsa.
Bayanai sun ce kafin waɗanda ke kusa a lokacin da abin ya faru su kai ɗauki, zakin ya riga da ya yi wa marigayin munanan raunuka wanda hakan ya yi ajalinsa daga bisani.
Tuni dai hukumar Jami’ar ƙarƙashin jagorancin Adebayo Simeon Bamire, ta bada umarnin kashe zakin. Haka nan, ta buƙaci a gudanar da bincike kan lamarin.
