News
Hukumar JAMB Ta Rufe Rijistar UTME Ta Shekarar 2024
DAGA UMAR IBRAHIM HOTORO
Hukumar shirya jarabawar shiga makarantun gaba da sakandire ta JAMB, ta ce rajistar jarrabawar shiga manyan makarantun gaba da sakandire ta shekarar 2024 (UTME) za ta kare ne a ranar Litinin 26 ga watan Fabrairu.
Hukumar ta bayyana hakan ne a cikin Bulletin ta na mako-mako na ofishin magatakardar da ke Abuja.
Jawaban da Ɗangote, Abdulsamad da Elumelu suka yi bayan ganawar su da Tinubu
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ta rawaito cewa an fara atisayen shekarar 2024 ne a ranar Litinin, 15 ga watan Janairu, a cibiyoyi sama da 700 na gwajin Kwamfuta (CBT) a fadin kasar.
Hukumar ta JAMB ta ce kawo yanzu kusan mutane miliyan biyu ne suka yi rajista, inda suka yi nasarar yin rijistar jarrabawar shekarar 2024, kuma jimillan mutane 260, 249 ne suka nuna sha’awar zana jarrabawar ta gwaji.
