News
Shugaba Tinubu ya ba da umarnin buɗe iyakokin Nijeriya da Nijar nan-take
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya bayar da umarni a buɗe iyakokin ƙasar da na Nijar nan take.
Mai magana da yan shugaban ƙasar Ajuri Ngelele ne ya sanar da hakan a ranar Laraba inda ya ce baya ga buɗe iyakokin, shugaban ya bayar da umarnin ɗage duka sauran takunkuman da Nijeriyar ta saka wa Nijar.
Kungiyar Manyan Ma’aikatan Jami’o’in Najeriya SSANU Da NASU Zasu Fara Yajin Aikin
Shugaban ya bayar da umarni kan a ɗage waɗannan takunkuman da aka saka wa Nijar nan take: –
1- Rufe iyakokin sama da ƙasa tsakannin Nijeriya da Nijar da kuma hana zirga-zirgar jiragen sama na kasuwanci wanda ECOWAS ta saka.
2- Dakatar da duka cinikayya tsakanin Nijeriya da Nijar, da dakatar da duka ayyukan da ke tsakanin Nijeriya da Nijar, daga ciki har da bai wa Nijar wutar lantarki.
3- Rike kadarorin Nijar a bankunan ƙasashen ECOWAS da dakatar da kadarorin Nijar da ke a bankunan kasuwanci.
4- Dakatar da ba Nijar duk wani tallafi na kuɗi da daina cinikayya da duk wasu cibiyoyi musamman EBID da BOAD.
5- Haramcin tafiye-tafiye ga jami’an gwamnati da iyalansu
Haka kuma Shugaba Tinubu ya bayara da umarnin cire takunkumin tattalin arziƙi kan Jamhuriyar Guinea
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
