News
Farfado Da Darajar Naira: Na Yabawa Shugaba Tinubu Bisa Namijin Kokarin Da Yake Wajen Ya Karyar Da Dalar Amurka —HON MUHAMMAD YUSUF INUWA (B.GWARZO)
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Dole ne Mu yabawa Shugaba kasa Bola Ahmad Tinubu bisa wannan namijin kokarin da yake wajen ganin ya karyar da darajar dakar Amurka domin farfado da darajar Naira a duniya .
Rahotanni na nuni da cewa wanda kuma Hakan ne zai sa yan Najeriya za su samu saukin rayuwa da kuma samun damar hada hadar kasuwancin su wanda hakan ya gagarin Gwamnatin baya da ta shude.
Haka zalika wanda kusan ma a yanzu zan iya cewa babu abun da talaka zai daga yace shine abun da ya amfana a lokacin da Gwamnatin baya da ta shude saide akasin hakada kuma banda tabarbarewar al,amura babu wani abun da Gwamnatin ta tsinana.
A sakamakon haka mu na kara kira ga Shugaba Tinubu da yakara jajircewa wajen ganin ya futar da yan Najeriya kunya duba da soyayyar da su ka nuna mai wajen dangwalame kuri,u tare da sama mu su dukan wani abun da yasan zai kara ciyar da Al, umma gaba batare da nuna banbanci Kabila, Addini Ko siyasa ba domin kara samar da hadin kai ga al, ummar Najeriya bakidaya.
