Connect with us

News

An Sake Dakatar Da Shugaban Jam’iyyar APC Na Kasa Abdullahi Umar Ganduje.

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Rikicin cikin gida da ya dabaibaye jam’iyyar APC a jihar Kano ya sake daukar sabon salo, inda wasu shugabannin jam’iyyar a matakin mazaba suka bulla, inda suka sake sanar da dakatar da mukaddashin shugaban jam’iyyar na kasa Abdullahi Umar Ganduje.

Advertisement

Solacebase ta ruwaito cewa sabon tsagin shugabancin jam’iyyar a mazabar Ganduje cikin karamar hukumar Dawakin Tofa sun ce su ne halastattun shugabannin jam’iyyar daaka zaba a 31 ga watan Juli, 2021.

Farfado Da Darajar Naira: Na Yabawa Shugaba Tinubu Bisa Namijin Kokarin Da Yake Wajen Ya Karyar Da Dalar Amurka  —HON MUHAMMAD YUSUF INUWA (B.GWARZO)

Da ya ke ganawa da manema labarai a Kano, Sakataren jam’iyyar na mazabar Ganduje Ja’afar Adamu, da ya yi magana a madadin sauran shugabannin jam’iyyar 11, ya ce dakatar da Ganduje a jam’iyyar ya zama wajibi biyo bayan zarginsa da yin ‘Anti Party’ wato yi wa jam’iyya zagon kasa musamman a zaben da ya gabata da ba ta yi nasara ba.

Advertisement

 

Ja’afar Adamu wanda dan’uwa ne na jini ga tsohon Gwamnan na Kano Abdullahi Ganduje, ya zargi mukaddashin shugaban jam’iyyar na kasa da kitsa wutar rikici da ta yi sanadiyar tabarbarewar lamurran jam’iyyar da yawa.

Advertisement

 

Sakataren jam’iyyar ya ma yi zargin cewa Abdullahi Umar Ganduje na ya biyan kudin harajin jam’iyyar na ‘statutory party dues’. Ya yi zargin cewa wadancan mutanen da ke kiran kansu shugabannin jam’iyyar APC a mazabar, na bogi ne.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending