Connect with us

News

Cuta da ba a san wace iri bace ta yi ajalin mutum 7 a Kaduna, ta kama wasu a Sokoto da Zamfara

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Hukumar Dakile Yaduwar Cututtuka ta Kasa NCDC ta bayyana cewa wata cuta da ta bullo a jihohin Sokoto da Zamfara da ba a san wace iri bace ta yi ajalin mutum 7 a jihar Kaduna.

Advertisement

Hukumar NCDC wanda ke fargaban cutar zata iya yaduwa na kokarin samo matakan gano ko mecece cutar da kuma hanyoyin dakile yaduwar cutar a wani taro da ta yi da kwamishinoni kiwon lafiya na jihohin Sokoto, Zamfara da Kaduna.

An Sake Dakatar Da Shugaban Jam’iyyar APC Na Kasa Abdullahi Umar Ganduje.

Premium Times ta ruwaito cewa Shugaban hukumar na jihar Sokoto Jude Idris ya ce tun bayan bullar cutar ranar 21 ga Maris 2024 mutum 196 ne suka kamu da cutar a kananan hukumomin Isa, Sabon Birni da Ilella dake jihar.

Advertisement

Idris ya ce hukumar za ta hada hannu da hukumar kula da ingancin magungunan da abinci ta kasa NAFDAC da hukumar gudanar da bincike ta kasa NIPRD domin gudanar da bincike don gano cutar da hanyoyin dakile yaduwar ta.

 

Advertisement

Ya yi kira ga sarakunan gargajiya da malaman addini da su hada hannu da su domin wayar da mutane kan cutar da hanyoyin da za su samu kariya daga kamuwa da ita.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending