Connect with us

News

Jahar Kano :Hukumar Kula da magunguna ta kashe kusan 10m domin Jin dadin ma,aikatan ta

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

 

 

 

 

 

Advertisement

 

A kokarin ta ina inganta jin dadin ma’aikatanta, Hukumar Kula da Magunguna ta Jihar Kano, karkashin jagorancin Pharm. Gali Sule, Darakta-Janar na Hukumar, yace sun kashe Naira miliyan 9.26 a lokacin shagulgulan bikin babbar Sallah

Shugaban hukumar ne ya bayyana hakan. Ta Bakin Aminu Datti, Shugaban Kwamitin Jin Dadi, yayin da yake gabatar da rahoton kwamitin ga Darakta Janar a ofishinsa.

A cewar shugaban kwamitin, an sayo shanu biyar, kuma an raba naman ga daukacin ma’aikatan hukumar, ciki har da wadanda ke aiki a ma’aikatun shiyya baya ga haka, an bayar da tallafin kudi domin tallafa wa ma’aikatan domin samun nasarar gudanar da bukukuwan Sallah.

Pharm Datti ya kuma kara da cewa an bayar da wannan tagomashinne ne domin zaburar da ma’aikatan da Kuma Kara inganta ayyukansu da sukeyi nayau da gobe

“Wannan shi ne karo na farko a tarihin DMCSA lokacin da aka bai wa mambobin ma’aikata kyaututtuka na kudi da nama a matsayin wani nau’i na motsa jiki,” in ji shi.

Advertisement

A nasa jawabin, Pharm. Gali Sule ya ce, “Asalin wannan karimcin shi ne inganta jin dadin ma’aikata da sauran masu ruwa da tsaki da ke tallafa wa Hukumar, musamman a wannan muhimmin aiki

Ya ce shirin ya yi daidai da ka’idojin Gwamna Abba Kabir Yusuf na taimakon mabukata da marasa galihu, domin gwamnatin jihar tana aiki ba dare ba rana domin inganta rayuwar jama’a.

“Mai Girma Gwamnan Jihar Kano Alh. Abba Kabir Yusuf a kodayaushe yana umurtar duk masu rike da mukaman siyasa a jihar da su kasance masu tausaya wa talakawa domin rage musu radadin da suke ciki musamman a wannan mawuyacin hali na tattalin arziki. Muna yin koyi da kyawawan halaye na mai martaba, shi ya sa muka fito da wanga tsari

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending