News
Sanata Ndume Ya Ki Amincewa Da Sabon Ofishin Da Aka Bashi A Majalisar Dattawa
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Sanata mai wakiltar Borno ta kudu a majalisar dattawan Nijeriya, Mohammed Ali Ndume, ya yi watsi da sabon ofishin da kwamitin ayyuka na majalisar dattawa ya bashi.
Ndume, a wata wasika da ya aike wa shugaban kwamitin ayyuka na majalisar dattawa a ranar Talatar nan, ya ce ofishin da aka ba shi bai nuna girmansa da matsayinsa a majalisar dattawa ba.
Wasikar mai dauke da sa hannun babban sakataren sa,Yati Shuaibu Gawu, ta ce: “An umurce ni da in sanar da ku cewa, Sanata Mohammed Ali Ndume, ya ki amincewa da ofishin da aka bashi mai lamba 3.10 da kwamitin ayyuka ya yi.
Jaridar INDA RANKA ta ruwaito kwanakin baya ne aka tube Ndume daga mukaminsa na babban mai tsawatarwa na majalisar dattawa, biyo bayan sukar da ya yi wa gwamnatin shugaban kasa Bola Tinubu.
