Connect with us

News

Kano: Jagoran Zanga-Zanga Ya Bayyana Bukatar Su

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

A dai-dai lokacin da matasan Najeriya ke shirin fara gudanar da zanga-zangar lumana daga ranar 1 ga watan Agusta, kungiyoyi a Kano sun ci gaba da bayyana ra’ayoyinsu kan wannan al’amari.

A wata hira da Premier Radio, Malam Adamu Mai AC ya bayyana cewa akwai bukatar gwamnati ta dawo da tallafin man fetur da ta cire.

Sanata Ndume Ya Ki Amincewa Da Sabon Ofishin Da Aka Bashi A Majalisar Dattawa

Malam Adamu ya jaddada muhimmancin wannan mataki ga rayuwar al’ummar kasa, musamman ma talakawa da ke fuskantar tsananin wahala sakamakon tsadar kayan masarufi.

Malam Adamu Mai AC ya tabbatar da cewa za su gudanar da zanga-zangar ne cikin lumana, kamar yadda aka tsara.

Ya ce, “Za mu fito ne da niyyar bayyana damuwar mu ga gwamnati, ba don mu tada hankali ko tada tarzoma ba.”

Advertisement

Ya kara da cewa ba za su lamunci duk wani yunkuri na daukar makami ko satar kayan jama’a ba a lokacin zanga-zangar.

Malam Adamu Mai AC ya yi kira ga al’ummar karamar hukumar Ungogo da su bayar da hadin kai domin ganin an samu nasarar gudanar da zanga-zangar ba tare da karya doka ko tada hankali ba.

A cewar sa, “Ya kamata mu nuna cewa muna da sanin ya kamata ta hanyar gudanar da zanga-zanga cikin kwanciyar hankali da bin doka.

”Zanga-zangar lumana da ake shirin gudanarwa a Kano na da nufin isar da sako ga gwamnati game da bukatar dawo da tallafin man fetur.

Jagoran zanga-zangar a Ungogo, Malam Adamu Mai AC, ya bayyana muhimmancin gudanar da wannan zanga-zanga cikin lumana, tare da neman hadin kan al’umma wajen tabbatar da cewa komai ya tafi yadda aka tsara.

Wannan rahoto ya kawo karshen yanayin da ake ciki a Kano, musamman ma a karamar hukumar Ungogo, inda matasa da shugabanninsu ke kokarin ganin an gudanar da zanga-zanga cikin kwanciyar hankali da lumana.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending