News
VIDEO: Jirgin Max Air Ya Yi Hatsari Ya Yin Sauka A Kano
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Wani jirgin Max Air daga Lagos ya yi hatsari ya yin sauka a Filin Jirgin Sama na Mallam Aminu Kano,
Hatsarin ya faru ne a ranar Talata da misalin ƙarfe 10:57 na dare.
Wani daga cikin fasinjoji ya tabbatar wa DAILY NIGERIAN cewa jirgin ya rasa tayar dogon hancinsa yayin sauka.
Gwamnoni Na Kokarin Sauya Sunayen Wadanda Za Su Samu Tallafin Kudaden Gwamnatin Tarayya —Minista
“Da zarar jirgin ya sauka, tayar ta fashe sannan ta kama wuta. Sai jirgin ya gangara ya tsaya a kan hanya,” in ji wani fasinja da ya nemi a sakaya sunansa.
A cewarsa, an gaggauta kwashe fasinjojin daga jirgin ba tare da rahoton samun rauni ba a cikinsu.
Cikakkun bayanai suna tafe…
Advertisements
