Connect with us

News

Gwamna Caleb Mutfwang Ya Sallami Kwamishinoni Biyar

Published

on

Mutfwang

DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA 

Gwamna Caleb Mutfwang na Jihar Filato ya sallami mambobi biyar na majalisar zartarwarsa.

Advertisement

Gwamnan ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da Sakataren Gwamnatin Jiha Samuel Jatau, ya fitar, amma bai bayyana dalilin korar su ba.

Watsi Da Irin Su El Rufai, Ba Alheri Ba Ne – Igbokwe

Waɗanda da abin ya shafa sun haɗa da Chrysanthus Dawam, kwamishinan Tsare-tsare da Tattalin Arziki, da Noel Nkup, kwamishinan Matasa da Wasanni, da Jamila Tukur, kwamishinar Yawon Buɗe Ido da Yawon Shakatawa, sai kuma Obed Goselle kwamishinan Kimiyya da Fasaha, da Sule Musa, kwamishinan Kasuwanci da Masana’antu.

Advertisement

Kazalika gwamnan ya amince da naɗa Sunday Alex daga Ƙaramar Hukumar Bassa, da Joyce Ramnap daga Langtang ta Kudu, da Sylvanus Dongtoe daga Shendam, da kuma Nicholas Baamlong daga Qua’an Pam, sai Cornelius Doeyok daga Ƙaramar Hukumar Qua’an domin maye gurbin waɗanda ya sallama.

Idan ba a manta ba a baya ma gwamnan ya dakatar da Dawam da Jamila na watanni uku bisa wasu dalilai da ba a bayyana ba, wanda a yanzu majiyoyi ke cewa sallmar tasu na da alaƙa da rashin aiki yadda ya kamata a shekarar da ta gabata.

Advertisement

Wannan ya janyo cece-kuce a cikin harkokin siyasa, inda masana ke hasashen yiwuwar sauya wasu mukamai da kuma tasirin sauyin a harkokin gwamnati.

 

Advertisement

 

LEADSHIP

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending