News
Ba Mu Fara Daukar Sabbin Ma’aikata Ba — Shugaban Hukumar KAROTA
DAGA MAIMUNATU BASHIR MUSA
Hukumar Kula da Zirga zirgar Ababen Hawa ta jiha KAROTA ta musanta jita-jitar da ake yadawa na fara daukar aiki a Hukumar
Shugaban Hukumar KAROTA Engr. Faisal Mahmud Kabir ne ya bayyana haka a jiya, ta bakin mai magana da yawon Hukumar Nabilusi Abubakar Kofar Na’isa
Gwamnatin Tarayya Ta Bayyana Cewa ‘Yan Najeriya Su Shirya Karin Kudin Wutar Lantarki
Ya ce Hukumar ta Kula da jita-jitar da ake yadawa na fara daukar sabbin Jami’an Hukumar wadanda hakan ba gaskiya ba ne
Sai dai ya ce Hukumar na tsaka da aikin tantance daukacin Jami’an KAROTA domin duba yuwuwar daukar sabbin Jami’an
A don haka Hukumar ke gargaðin jama’a, da su guji yada jita-jitar fara daukar sabbin Jami’an KAROTAR
Hukumar ta ce duk wanda ta kama da hannu wajen yada jita-jitar zata gurfanar da shi gaban sharia domin ya girbi abinda ya shuka
Engr. Faisal ya roki jama’a da su yi gaggawar sanar da Hukumar ta KAROTA ko ofishin Yansanda mafi kusa wanda duk aka samu yana yada jita-jitar
A karshe Hukumar ta ce idan za a dauki sabbin Jami’an za a sanar a Hukumance ta kafafen yada labarai
-
News4 days agoWasu Ƴan Daba Sun Kai Farmaki Kasuwar Siyar Da Wayoyi Ta Farm Center Dake Kano
-
News6 days agoWasu Fusatattun Matasa Sun Ƙona Mutum Uku Har lahira A Filato
-
News6 days agoAbin Takaici Ne A Kyale Mata Su Cire Wandunan Da Aka Basu Akan Titi Suna Dagawa A Cikin Al’ummar Da Ke Alfahari Da Kunya Da Addini
