News
Barawo Ya Hadiye Dan Kunnen Zinare Na Naira Biliyan 1
Jami’an tsaro a birnin Orlando sun cafke wani mutum mai shekaru 32, Jaythan Lawrence Glider, bayan ya sace ‘yan kunne biyu na zinare masu darajar sama da dala 769,000 (kimanin naira biliyan 1.17), daga babban kantin kayan ado na Tiffany & Co. dake cikin Millenia Mall.
Rahotanni sun bayyana cewa Glider ya fake da matsayin wakilin ɗan wasan ƙwallon kwando na Orlando Magic, wanda hakan ya ba shi damar shiga sashen kayan ado masu tsada. Daga nan ya wawuri ‘yan kunnayen ba tare da an gano shi ba a lokacin.
Babban Sufeton Ƴan Sandan Najeriya Ya Janye Sammacin Da Ya Yi Wa Sarki Muhammadu Sanusi II
Bayan kisan laifin, jami’an ‘yan sanda sun cafke Glider a kan titin Interstate 10 a gundumar Washington, inda aka gano cewa yana da sammaci har guda 48 daga jihar Colorado.
Abin mamaki ya bayyana lokacin da aka kai shi gidan yari, inda ya tambayi ma’aikatan, “Shin za a tuhume ni da abin da na hadiye?” Wannan tambaya ce ta sanya aka gudanar da bincike a jikinsa, wanda ya kai ga gano cewa ya hadiye ‘yan kunnayen zinaren da ya saci.
Jami’an tsaro sun tabbatar da cewa kayan da aka sace na da matukar daraja, kuma suna ci gaba da gudanar da bincike domin gano cikakken bayani kan lamarin da kuma gano abokan aikinsa idan suna da hannu.
Wannan lamari ya kara bayyana irin sabbin dabarun da barayi ke amfani da su, lamarin da ke kara tayar da hankalin jami’an tsaro da masu kasuwanci a duk fadin duniya.
