News
Kotu Ta Daure Ango Amuscap Wata 6 Saboda Wulakanta Naira A Bikinsa
A wani lamari da ya tayar da kura a Kano, babbar kotun tarayya da ke birnin ta yanke hukuncin daurin watanni shida ga wani matashi mai sana’ar kwalliya, Abdullahi Musa Huseini, wanda aka fi sani da Amuscap, bisa laifin wulakanta takardar Naira yayin bikin aurensa.
Mai shari’a S.M Shuaibu ne ya zartar da hukuncin bayan wanda ake tuhuma ya amsa laifin da ake zarginsa da shi, wanda ya shafi cin zarafi da lalata kudin Najeriya.
Gwamnoni Sun Hana Shugabannin Kananan Hukumomi Buɗe Asusu A CBN
An kama Amuscap ne bisa wasu bayanai na sirri da suka nuna cewa ya yi liki da takardun Naira a wurin shagalin bikinsa – wani abu da hukumar EFCC ke bayyana a matsayin sabawa doka da kuma ƙoƙarin lalata darajar kudin ƙasa.
Lauyan gwamnati, Zarami Mohammed, ya gabatar da bayanai da hujjoji a gaban kotu, lamarin da ya tabbatar da laifin wanda ake tuhuma ba tare da tantama ba. Mai shari’a Shuaibu ya yanke hukuncin daurin watanni shida ba tare da zabin biyan tara ba, yana mai jaddada cewa wannan hukunci na zaman darasi ne ga sauran ‘yan ƙasa.
EFCC ta sha nanata muhimmancin girmama kudin kasa tare da gargadin cewa duk wanda aka samu da irin wannan laifi ba zai tsira da sauki ba.
-
News2 days ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
