Connect with us

News

H-S Biggy Foundation Ta Ba Da Tallafin Kuɗi Ga Yara 100 Masu Fama Da Cututtuka A Asibitin Kano

Published

on

IMG 20250630 WA0007

Kungiyar agaji ta H-S Biggy Foundation ta ba da tallafin kuɗi ga yara 100 da ke fama da cututtuka daban-daban a Asibitin Kananan Yara na Sheikh Isyaka Rabiu (Paediatric Hospital)dake birnin Kano.

A wata sanarwa da Sakataren kungiyar, Kabeer Abdullahi ya fitar, ya bayyana cewa wannan shiri na tallafawa marasa lafiya a asibiti shi ne na farko da kungiyar ta gudanar, duk da cewa ta saba ba da tallafi a gidaje da makarantu.

Advertisement

Farfesa Gwarzo ya taya Hadiza Ma’aji murnar kaiwa ga matakin Farfesa da Jami’ar ABU ta yi mata

“Mun yanke shawarar ziyartar asibitin domin mu ga yanayin da marasa lafiya ke ciki. Mun ga cewa akwai buƙatar taimako sosai, don haka muka himmatu wajen ba da gudummawar mu, ko da yake ba mu da wadatar kuɗi,” in ji Kabeer.

Ya kuma yi kira ga gwamnatin jihar Kano, masu zaman kansu, da masu hannu da shuni su kara ba da tallafi ga irin wadannan asibitoci, musamman ma kananan yara marasa galihu.

Advertisement

Kofar mu a bude take ga duk wanda yake son taimakawa. Muna karfafa mutane su zo su ba da gudummawa, ko da ta hanyar shawarwari da kaimi,” ya kara da cewa.

H-S Biggy Foundation na daga cikin ƙungiyoyin agaji da ke aiki don inganta rayuwar marasa galihu a jihar Kano da sauran sassan Arewacin Najeriya.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending