News
KAROTA Ta Haramtawa Manyan Motoci Hawa Gadojin Sama A Kano
Hukumar Kula da Zirga-zirgar Ababen Hawa ta Jihar Kano (KAROTA) ta sanar da haramta hawa gadojin sama da ke birnin Kano ga manyan motocin ɗaukar kaya, tare da fara cafke masu karya wannan doka.
Mataimakin Shugaban hukumar, Auwal Lawan Aranposu ne ya bayyana hakan a hirarsa da Arewa Updates a ranar Litinin, 14 ga Yuli, 2025.
Yadda makiyaya ke gwagwarmayar rayuwa a yayin da ake fama da sauyin yanayi
Aranposu ya bayyana cewa tuni hukumar ta kama wasu daga cikin manyan motocin da suka karya doka ta hanyar hawa gadar sama, kuma suna hannun KAROTA domin ɗaukar matakin da ya dace.
Ya ce, “Mun fara cafke motocin da suka karya doka, kuma za mu ci gaba da sanya ido domin ganin an bi wannan ƙa’ida da aka shimfiɗa. Doka za ta yi aiki da duk wanda aka samu da laifi.”
Ya kuma ja kunnen direbobi da masu manyan motoci da su guji hawa gadojin sama a fadin Kano, yana mai cewa wannan mataki na daga cikin kokarin gwamnatin jihar na tabbatar da tsaro da kyakkyawan tsari a harkar zirga-zirga a birnin.
A cewar KAROTA, gadojin sama a Kano an gina su ne domin amfanin kananan motoci da masu tafiya a ƙasa, ba don manyan motocin ɗaukar kaya ba.
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
