News
Al’ummar Kofar Kaza A Kano Sun Gudanar Da Sallar Qunut Kan Zargin Wani Hakimi Da Mamaye Filayensu
Wasu mazauna kauyen Fancan Kwari da ke unguwar Kofar Kaza a karamar hukumar Dawakin Kudu, jihar Kano, sun gudanar da sallar Qunut da yankan rago a matsayin neman taimakon Ubangiji, kan zargin wani hakimi da mamaye filayen da suka gada daga kakanninsu. Al’ummar sun bayyana cewa hakimin Gajere da ke karamar hukumar Bunkure, Malam Abubakar Isyaku, na sayar da filayensu ga masu kudi daga birni, duk da cewa filayen na cikin yankin Dawakin Kudu ne, ba Bunkure ba.
Shugaban al’ummar, Usman Uba, wanda ya taba kasancewa kansila a yankin, ya ce an dade ana kokawa da wannan batu, kuma yanzu abin ya kai makura. Ya ce, “Filayen nan mu ne da kakanninmu suka gada, muna noma a kansu domin mu samu abin ciyar da iyalanmu. Yanzu ga wani yana zuwa yana siyar da su ga wanda suka fi karfinmu. Wannan zalunci ne.”
Ganawar Sirri: Kwankwaso ya gana da Shugaba Tinubu a fadar shugaban kasa
Wani mazaunin kauyen, Malam Dalliti Awala, ya ce sun yi mamakin yadda wani hakimi daga wata karamar hukuma ke shigowa yankinsu ba tare da izini ba, yana sayar da filaye da suka mallaka tsawon shekaru. Ya ce ba za su zura ido suna kallon abin yana ci gaba ba, don haka suka nemi taimakon Allah sannan suka roki gwamnati ta shigo cikin lamarin.
Da aka tuntube shi, hakimin Gajere, Malam Abubakar Isyaku, ya musanta zargin da ake masa, yana mai cewa filayen mallakin gwamnatin tarayya ne. Sai dai ya ki yin karin bayani kan batun sayar da filayen, kuma daga bisani ya kashe wayarsa.
Mazauna Fancan Kwari sun bukaci gwamnatin jihar Kano da hukumomin tsaro da su gaggauta shiga tsakani domin dakile abin da suka kira barazana ga rayuwarsu da makomar ‘ya’yansu. Sun ce filayen su ne kadai hanyar samun abin dogaro da kai da kuma ci gaba da rayuwa cikin mutunci.
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
