Connect with us

News

‎Yaduwar Al’adar ‘Signing Out’ A Makarantun Sakandare: Gazawar Iyaye Ko Hukumomi?

Published

on

FB IMG 1753655134805

A baya, an fi sanin al’adar “signing out” da manyan makarantu kamar jami’o’i da kwalejoji — inda ɗalibai ke yin rubuce-rubuce da zane a jikin tufafi ko fata a matsayin nuni da sun kammala karatu a jihar Kano. Sai dai a yanzu, wannan al’ada ta fara shigowa makarantun sakandare, lamarin da ke ƙara tayar da kura a kafafen sada zumunta da tsakanin masu fashin baki a harkar tarbiyyar matasa.

‎A cikin hotuna da bidiyoyi da suka karade shafukan sada zumunta a kwanakin nan, an ga yara maza da mata ‘yan sakandare — wasu ma ƙasa da shekaru 15 — suna barin jiki domin a  rubuta musu a tufafi ko kai tsaye a fatar jikinsu.

Advertisement

‎A wasu lokuta, ana ganin wasu ƴan mata na kokarin hana a taɓa su ko rubuta musu, amma ana tilasta musu hakan da ƙarfin tsiya. Wasu kuma da kansu ke bayar da jiki cikin annashuwa da dariya, alamar yadda abin ke zama ruwan dare a wasu makarantu.

Ɓarayi Sun Kai Hari Gidan Rediyon Tarayya, Sun Sace Kayan Aiki

‎Wata  malamar makaranta a jihar Kano, Khadija Nasser Musa , ta ce irin wannan al’ada ba ta dace da matakin yara ‘yan sakandare ba. “Wannan al’ada ta manya ce, kuma ita ma tana da tsaiko. Amma yanzu ganin yara ƙanana suna aikata hakan, musamman a bainar jama’a, abin damuwa ne matuƙa,” in ji ta.

Advertisement

‎A cewarta, wannan al’ada ta “signing out” da ta fara zama ruwan dare a sakandare na nuni da gibi a tsakanin iyaye, malamai da hukumomin makarantu. “Idan duka waɗanda ke da alhakin kula da tarbiyyar yara suka ci gaba da yin shiru, za mu wayi gari yara sun ɗauki wannan a matsayin dabi’ar al’ada,” in ji shi.

‎Masu fashin baki na ganin cewa rashin kulawa daga iyaye, da rashin isassun dokoki daga makarantu da hukumomin ilimi, na daga cikin manyan dalilan da ke ba wa wannan al’ada damar kafe kafa.‎

Advertisement

‎Kwararru a fannin ilimi na cewa lokaci ya yi da gwamnati za ta fitar da tsari da doka da za ta hana irin wannan taron a makarantu, tare da wayar da kan iyaye da ɗalibai kan yadda ya kamata a gudanar da murnar kammala makaranta.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending