News
CAC Ta Ba Kamfanoni 100,000 Wa’adin Watanni Uku Ko Ta Goge Sunayensu Daga Rajista
Hukumar Rajistar Kamfanoni (CAC) ta bayyana cewa za ta soke rajistar kamfanoni sama da 100,000 da suka gaza gudanar da harkokinsu na kasuwanci tsawon lokaci, musamman wadanda suka daina aiki sama da shekaru 10 ba tare da cikawa wasu muhimman sharuddan da doka ta gindaya ba.
Wannan na kunshe ne a wata sanarwa da hukumar ta fitar a ranar Litinin, inda ta ce matakin na daga cikin kokarinta na tsaftace tsarin rajista tare da tabbatar da cewa sai kamfanonin da ke da sahihiyar mu’amala da doka ne kawai za su ci gaba da kasancewa a cikin rijistar hukumarta.
Matashi Yayi Ajalin Surukarsa Saboda Matsin Lamba Kan Sha’anin Aurensa
A cewar CAC, an gano cewa wadannan kamfanonin sun gaza sabunta rajistarsu da kuma biyan kuɗaɗen da ake bukata a ƙarƙashin dokar CAMA, wanda hakan ke nuna cewa ba su da wani tasiri a harkokin tattalin arziki da kasuwanci na ƙasa.
Hukumar ta bayyana cewa ta bai wa kamfanonin da lamarin ya shafa wa’adin kwanaki 90 – wanda yake daidai da watanni uku – domin su sabunta rajistarsu, su biya duk wasu kuɗaɗen da ake binsu, tare da mika sahihan bayanai game da matsayin kamfanin nasu.
Ta kuma bukaci kamfanonin da su tura bayanansu zuwa adireshin imel na musamman da aka ware domin wannan aiki, wato activation@cac.gov.ng, kafin wa’adin ya cika.
A cewar CAC, matakin zai taimaka gaya wajen tabbatar da gaskiya da tsabta a harkokin rajista, da kuma kare tattalin arzikin ƙasa daga miyagun ayyuka kamar safarar kuɗi da wanke jari ta hannun kamfanoni na bogi.
Hukumar ta jaddada cewa ba za ta jinkirta soke duk wani kamfani da ya kasa cikawa sharuddan da aka gindaya ba bayan karewar wa’adin da aka bayar.
