News
Gwamna Abba Ya Naɗa Sabon Shugaban Hukumar Yaƙi Da Rashawa Ta Jihar Kano
Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya mika sunan Comrade Sa’idu Yahya ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatar da shi a matsayin sabon shugaban Hukumar Karɓar Ƙorafe-ƙorafe da Yaƙi da Rashawa ta jihar, wato PCACC.
A wata sanarwa da Daraktan Yaɗa Labaran Gwamnatin Jihar, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a ranar Alhamis, ya ce Yahya ya shafe kusan shekaru 18 yana aiki a fannin yaki da cin hanci, musamman a hukumar ICPC.
Gine-Gine a Kan Hanyoyin Ruwa Ne Ya Haddasa Ambaliyar Maiduguri – NEMA
A cewarsa, Yahya ya rike mukamai daban-daban a fannin bincike, gano kadarori, da kuma sa ido kan ayyukan gwamnati da na ‘yan siyasa.
Gwamna Abba ya ce gogewar Yahya za ta taimaka wajen ƙarfafa aikin hukumar, musamman wajen bin diddigin kadarorin da aka mallaka ta hanyar cin hanci.
A wani mataki na daban, gwamnatin Kano ta nada Barrister Hafsat Ada’u Kutama a matsayin sabuwar Sakatariyar PCACC da kuma mai ba da shawara ta musamman kan harkokin doka.
Tsohon mai rike da mukamin, Barr. Zaharadden Hamisu Kofar Mata, an mayar da shi ma’aikatar shari’a domin ci gaba da aikinsa a can.
